Ministan Matasa da wasanni na Najeriya Solomon Dalung yace shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana gab da dawo Najeriya bayan samun sauki da yake ci gaba da yi game da jinyar data kai shi Birnin London.
A hirar wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Andulwahab Mohammed da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Gombe DSP Obed Mary Maglum ta tabbatar da aukuwar lamarin da kuma iri matakan da aka dauka domin kawar da matar kan hanya.
Gwamnatin kasar Cameroon ta yi kra ga ‘yan kasar dake kasar waje dasu dawo gida domin kafa masanaantu.
Duk da ziyarar da yake yi a Paris dake Faransa, birnin da kasashe 195 suka kulla yarjejeniyar daukan matakan yaki da sauyin yanayi, shugaban Amurka Donald Trump bai nuna wata alama dake nuna zai sauya matsayar da ya dauka kan janye Amurka daga shirin ba.
Bayan da aka yanke mai hukuncin daurin shekaru 9.5 a gidan yari saboda samunsa da laifin aikata rashawa da kuma halalta kudaden haram, tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya ce zai daukaka kara.
Bayan wani hari da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai a Maiduguri dake jihar Bornon Najeriya dake arewa maso gabashin kasar, hukumomin tsaro sun fayyace adadin mutanen da suka mutu ya zuwa yanzu.
Mataimakin shgugaban majilisar dokokin Jamhuriyar Niger Iro Sani yace lallai an kawo batun gyaran fuska akan hukumar zabe sabo da yanzu hukumar zaben kasar ta din-din-din ce, ba wai sai zabe ya karato ba a girka hukumar zabe kuma mutanen dake cikin ta suna da wa’adi na shekaru 6.
Masu nazari sun kirkiro da wani sabon gwajin jinni da ka iya taimakawa wurin gano cutar daji dake kama kundun dan adam wato “Pancreatic Cancer” a turance da wuri wuri, wannan cuta tana cikin cutauttuka mafi hadarin.
Majalisar Dinkin Duniya tace ta gano wasu manyan kaburbura 38 da aka bisa mutane a ciki a tsakiyar Congo inda rikici ya kashe dubban mutane tun daga Agustan bara. Wannan ne ya kai adadin manyan kaburburan da aka gano a yankin Kasai zuwa tamani, a cewar rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo a jiya Laraba. Majalisa Dinikin Duniya ta kiyasta cewar mutane miliyon guda da dubu dari uku ne suka suka rasa muhallansu suna cikin gida sa’annan wasu dubu dari uku kuma suka arce zuwa makwabciya Angola tun barkewar rikicin a cikin watan Agusta. Kashe sarkin wata kalbila da yan sanda da sojoji suka yi shine ya tado da hare haren ramuwar gayya da wasu hare haren kuma tsakanin yan bindiga masu biyayya ga sarkin Kamuina Nsapu da dakarun tsaron gwamnati.
Yayin da ake shirin fara jigilar alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana, kwamaitin dake kula da ayyukan hajjin a majalisar wakilan kasar ya ce zai kara gabatar da bukatar neman a rage kudin wannan farali wanda aka kara a wannan shekara.
A wani taron manema labarai da kungiyoyin suka kira a babban birnin tarayyar Najeriya sunce har yanzu ana zaman dar-dar duk ko da jamiaan tsaron da aka kai Mambila a karamar hukumar Sardauna dake jihar ta Taraban
Wannan nema dai karon farko da wani wanda ba jami’in gwamnati ba ko kuma dan siyasa ke kai tallafi ga wadanda rikicin tsaunin mambilan ya shafa, inda shahararren dan kasuwan Aliko Dangote ya bada tallafin naira miliyan hamsin ga gwamnatin jihar a matsayin gudumawa.
Kasar Saudiyya da kawayenta da suke rikici ta fuskar difilomasiyya da Qatar, yau Litinin, suka kara wa'din da suka baiwa Qatar da sa'o'i 48 ta cika sharudda da suka gindaya mata.
Jiya Lahadi a Iraqi, wani dan kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 14, a wani sansanin 'yan gudun hijira da tashe tashen hankula a cikin kasr suka raba su da muhallansu.
Jami'ai a kasar Indonesia sun fada yau Litinin cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu, dauke masu aikin ceto, da sojojin ruwa na kasar su hudu, yayi hadari
A jiya lahadi ne Amurka ta dage dokar hana shiga cikin jirigin sama da komputar hanu daga Abu Dhabi, helkwatar hadaddiyar daular kasashen larabawa
An samu ambaliyar ruwa a yankin Kumasi dake gundumar Ashanti na kasar Ghana, hakan ko ya biyo bayan ruwan sama da akayi har na tsawon saoi 3 ba kakkautawa kamar da bakin kwarya.
Wanda dai ake tsare dashi na baya-bayan nan shine Ibrahim Bana kakakin matasan na jamiyyun adawa bayan da kungiyar alkalan Jamhuriyar Niger SAMAN ta shigar da kara akansa cewa yaci zarafin alkalai akan shafin sa na sada zumunta.
Kamar dai yadda alkalumma ke bayyanawa fiye da gadoji biyar ne mayakan Boko Haram suka lalata a arewacin jihar Adamawa,wato kama daga na Maiha har zuwa na yankin Madagali, da Micika .
A karon farko mahukuntar kula da ayyukan Hajji na Najeriya sunyi bikin cika shekaru 10 da kafa hukumar.
Domin Kari