Yayin da batutuwan siyasa ke dada jan hankali a Najeriya, kasar da ke shirin zaben shugaban kasa badi, tsohon Shugaban kasar, Ibrahim Babangida, ya yi kira ga 'yan siyasa da su sa kasar gaba da kansu, sannan ya ce shi bai goyon bayan tsarin karba karba; dan Najeriya da ya dace ne kadai gwaninsa.
Abuja, Najeriya.
Lamarin ya auku ne da yammacin ranar Talata, a lokacin da wasu matasa dauke da makamai na gargajiya suka kai farmaki a gidan tsohon kwamishinan muhalli na jihar Sokoto.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan Na Shekarar 2022.
• Dan wasan Super Eagles na Najeriya ya kaddamar da gidan marayu a Legas • Newcastle tana zawarcin shahararren dan wasan Najeriya • Liverpool da Manchester United suna yakin samun matashin dan wasan Barcelona • Za’a soma fafata zagayen ‘yan 16 na gasar zakarun turai
Mai martaba sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya ce masarautarshi ba ta sayar da mukami ga mutane, sai dai ta na bayar da sarauta ga mutane ne bisa cancantarsu. Sarkin ya sanar da hakan ne yayin da ya nada ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi a matsayin Dan Amanar Daura.
A can baya shugaba Buhari ya ki rattaba hannun amincewa da sabuwar dokar zaben da majalisar dokoki ta gabatar masa, saboda a ganinsa, ta saba wa tsarin dimokaradiyya da ya ba da dama da zabin hanyoyin tsayar da 'yan takara.
Kasar Senegal ta sha da kyar a wasanta na farko da Zimbabwe na gasar kwallon kafar cin kofin nahiyar Afirka da ake fafatawa a kasar Kamaru.
Hakan na nufin Eto'o, wanda ya lashe lambar gwarzon dan kwallon Afirka har sau 4, zai jagoranci hukumar kwallon kasar ta kamaru na tsawon wa’adin shekaru 4.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sanusi Buba, ya tabbatar da rasuwar kwamishinan da daren jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan marigayin da ke gidajen estate din Fatima Shema kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito.
Wannan lamari na zuwa ne kwana 2 bayan da wata babbar kotu a Abuja ta tabbatar da shugabannin jam’iyyar ta APC da aka zaba daga bangaren Sha’aban Sharada da Malam Shekarau, a zaman halatattun zababbin shugabannin APC.
A daren Litinin ne ake bikin karama gwarzayen shekara a haujin kwallon kafar duniya da aka fi sani da Ballon d’Or, a birnin Paris na kasar Faransa.
Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta sallami mai horar da 'yan wasanta Ole Gunnar Solskjaer, yayin da ake rade-radin yiwuwar maye gurbinsa da kocin PSG Mauricio Pochettino ko tsohon kocin Real Madrid Zinadine Zidane
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaye kallabin sababbin kudurorin Amurka sa'adda yake jawabi ga jami'an diflomasiyya da na gwamnatoci a sakatariyar kungiyar raya kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ya ke ci gaba da ziyara
Amurka da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aiki tare a bangarori da dama, inda kasar ta Amurka ta yi alkawarin taimaka wa Najeriyar wajen shawo kan wasu daga cikin dinbin matsalolin da take fuskanta.
Soludo yayi takara ne a karkashin inuwar jam’iyyar APGA mai mulkin jihar, inda ya kayar da abokan takararsa 18, manya daga cikinsu, Valantine Ozigbo na jam’iyyar PDP, da kuma Andy Uba na jam’iyyar APC.
Domin Kari