Shaidun gani da ido sun ce bayan harbin kan mai uwa da wabi da ‘yan bindigar suka yi a wajen taron na dan kankanin lokaci da yayi sanadiyyar mutuwar sarakunan, nan take kuma suka bar wajen ba tare wani jinkiri ba.
A ranar Assabar da ta gabata ne dai kungiyar ta NUPENG ta ba da sanarwar cewa direbobin tanka masu jigilar man fetur za su soma yajin aiki a yau Litinin, sakamakon mawuyacin halin da titunan kasar suke ciki, da kuma wasu korafe-korafe.
Wasu mazauna jihar Zamfara da suka kunshi kabilu daban-daban sun hada kai guri daya suka gudanar da addu’ar neman dauki kan matsalar tsaro da ke kara kamari a jihar.
Mba ya ce “an riga an rusa SARS, kuma ba za’a sake dawo da ita ba ta ko wace siga.”
"Rahotannin da hukumar ke samu na nuni da cewa babbar manufar wasu ‘yan ta da kayar baya, shi ne hana gudanar da zaben gwamnan jihar ta Anambra ko ta halin yaya."
Dokar ta tilastawa dukkan jihohi da su hada da kason kudaden bangaren shari’a da na majalisun dokoki a cikin kasafin kudinsu.
“Kama Nnamdi Kanu da Sunday Igboho da aka yi a kwanan nan, da kuma binciken da ake ci gaba da yi, sun bayyana cewa akwai wasu manyan mutane da ke daukar nauyinsu, ciki har da wani da aka gano cewa dan majalisar dokokin Najeriya ne mai ci yanzu.”
Duk da yake dai ba’a kai ga kama wadanda ke da hannu akan kisan ba, babban tsohon na hannun daman Nnamdi Kanu, Uche Mefor, ya bayyana kisan da cewa aiki ne na baya-bayan nan na kungiyar ta IPOB, zargin da kungiyar ta musanta.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Dr. Akunyili ne da yammacin ranar Talata, a Umuoji da ke yankin karamar hukumar mulki ta Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana sabon sarkin Gaya, da zai maye gurbin marigayi Alhaji Ibrahim Abdulkadir, wanda Allah ya yi wa rasuwa a makon da ya gabata.
Wata zanga-zangar nuna damuwa akan kara tabarbarewar sha'anin tsaro a garin Isa da ke jihar Sokoto, ta rikide zuwa tarzoma, lamarin da ya yi sanadiyyar kai farmaki tare da kona gidajen kwamishinan lamurran tsaro da kuma na basaraken garin na Isa.
Malami ya ce a halin da ake ciki na gudanar bincike, zai iya kasancewa riga malam masallaci a bayyana sunayen wadanda ake zargi, wanda kuma kan iya wargaza nasarar da ake ta samu a halin yanzu a haujin yaki da kalubalen tsaro a kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar dattawan Arewa ta ke ci gaba da jaddada matsayarta kan rashin goyon bayan tsarin mulkin karba-karba da ake fafutukar yi, domin baiwa kudancin kasar karbar shugabanci a shekarar 2023, bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Wata sanarwa da mai bai wa gwamna Tambuwal shawara kan lamurran watsa labarai Muhammad Bello ya fitar, ta ce sabuwar dokar rufe kafofin sadarwa da ta soma aiki a ranar Litinin, ta shafi kananan hukumomin mulki 14 na jihar.
Wadanda ake zargi da kisan dan Sanata Bala Na’Allah sun shiga hannu, sun kuma bayyana dalili da kuma yadda suka kashe Abdulkarim Bala Na’Allah.
Takardar ta ci gaba da cewa matakin na shugaba Congo na taya Pantami murna, tamkar takala ne da raina shugabancin CAN na kasa, haka kuma ba ya wakiltar matsayar shugabannin kungiyar.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Femi Fani-Kayode ya ce akwai yiwuwar wasu gwamnoni 3 na PDP su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da aukuwar harin bam da jirgin saman yakin soji ya kai kan al'ummar kauyen Buhari, duk kuwa da cewa rundunar sojin saman Najeriya ta musanta aukuwar harin.
A cewar ministan, hukumomin tsaro sun kammala bincikensu kuma tuni sun mika shawarwari da suka bayar ga hukumomin da ya kamata.
Kungiyar 'yan kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta ce dokar zama gida da kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biayafara wato IPOB ta kakaba a ranakun Litinin da Talata tana kokarin kassara tattalin arziki da kuma ilimi a yankin Kudu maso gabashin Najeriya.
Domin Kari