An saki sojoji 45 da aka yanke wa hukunci, aka kuma tsare su tsawon shekaru 7 da suka gabata, sakamakon zanga-zangar da suka yi ta korafin rashin isassun makamai, a yayin da suke fagen dagar yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.
"Lokaci ya yi da hukumar ta kwastan za ta gane cewa yadda jami’anta ke aiki a jihar Katsina ya saba doka, kuma ba za’a lamincewa haka ba."
Yana da matukar wahala jama’a su karbi mutanen da suka kashe musu iyaye da ‘ya’ya da sauran ‘yan uwa, haka kuma idan kuma aka ki karbar mayakan da suka tuba suka mika, suna iya komawa kungiyar ISWAP, su kuma kara yawan mayakanta a cikin daji.
Wata tawagar matasan lauyoyi 31 na Arewacin Najeriya sun kuduri aniyar taimakawa wajen goyon baya da kariyar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, da ke fuskantar tuhuma a kasar Amurka.
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar Bayelsa ta Yamma Henry Dickson, ya musanta zargin wawure baitul malin jihar a yayin da yake kan kujerar gwamnan jihar.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus ya tsira daga yunkurin kawarda shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar da wasu ‘yan kwamitin zartarwa suka yi, a cikin wani rikicin cikin gida da ya barke a jam’iyyar.
Ministan al’amuran kasashen wajen Najeriya Geofferey Onyeama, ya ce gwamnatin Najeriya ta bukaci hukumomi a Indonesia su dau mataken ladabtarwa akan jami’anta da suka ci zarafin jami’inta na diflomasiyya a Jakarta.
Rahoton hukumar lafiya ta duniya ya nuna cewa Najeriya kadai ce take da kashi 27 cikin dari na dukan cutar maleriya a duniya, haka kuma kasar ce ke da kashi 23 na adadin mutanen da cutar ke kashewa a fadin duniya.
Baya ta haihu a shirye-shiryen dan wasan kasar Argentina Lionel Messi, na komawa kungiyar PSG ta kasar Faransa, a yayin da lauyoyin Barcelona suka garzaya kotu, domin hana komawar ta shi.
Rahotanni daga jihar Naija da ke Arewacin Najeriya sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan watsa labarai na jihar, Mohammed Sani Idris.
Wata babbar kotun jihar Adamawa da ke Yola, ta ba da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 30, bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 2 da haihuwa fyade.
Wata sabuwar dambarwa ta kunno kai a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, sakamakon murabus da wasu shugabannin jam’iyyar 7 na kasa suka yi daga mukamansu.
Wasu gaggan ‘yan bindiga sun gamu da ajalinsu, a yayin karbar kudin fansar wani da suka sace a jihar Taraba.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya – EFCC ta musanta ikirarin ma’aboci shafin yanar gizo na Instagram, Ismaila Mustapha, cewa hukumar ta shawarce shi da ya rage kwaramniya.
“A karkashin jagorancin Mai Mala Buni, jam’iyyar APC ba ta da shugabanni na kasa, haka kuma duk wasu taruka da zaben shugabanni da aka gudanar a karkashinsu ba halatacce ba ne.”
Manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun dinke barakar da ke tsakaninsu.
“Kafafen yada labarai da dama sun buga labarin, amma me ya sa babu wanda ya rubuta wannan kwatancen sai Sahara Reporters? Wannan kage ne kawai, domin sam ba shi ne gangar jikin kan labarin da suka wallafa ba” in ji Afenifere.
To sai dai a yayin da dalibai 3 da suka tsero daga ‘yan bindigar suka sami isa gida, na hudun su ko rashin sa’a ya yi domin kuwa wani dan bindigar ya kuma kame shi sa’adda yake gudun tsira.
Gwamnonin jihohin Najeriya na jam’iyyar PDP sun bayyana cewa suna nan kan bakan su na goyon bayan tsarin amfani da na’ura wajen tattarawa da aikewa da sakamakon zabe.
A ranar Litinin aka yi zaman sauraren karar jagoran kungiyar IPOB Nnamdi Kanu a babbar kotun tarayya ta Abuja, amma kuma ba'a je da shi kotun ba.
Domin Kari