Noma Tushen Arziki
Kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bam a kasuwa Magali dake jahar Adamawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 9 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya.
Gwamnatin jahar Adamawa ta raba Taraktocin noma sama da ‘dari ga kananan hukumomin jahar 21, domin bukasa harkar noma a jahar.
Tagwayen bama bamai sun tashi a lokacin da ake hada hadar cin kasuwa a garin Madagali dake jahar Adamawa, wanda kawo yanzu babu masaniyar ko mutane nawa ne suka rasa rayukansu.
Shugaba Mohamadu Buhari yayi wa takwarorinsa na nahiyar Afirka albishir din cewa a watan Disambar nan ana sa ran sojojin Najeriya dana makwabtan kasar zasu afkawa dajin Sambisa domin gamawa da matsalar ‘yan Boko Haram lokaci daya.
Yanzu haka dai ana zaman ‘dar ‘dar a kasar Ghana biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar jiya Laraba, wanda yanzu haka ake jiran sakamakon zaben daga hukumar zabe ta kasar.
Makarantar makafi dake birnin Konni na fama da matsalar rashin samun dalibai, domin iyayen yara na turasu bara maimakon makaranta.
Mutanen dake zaune a garuruwan zagayen madatsar ruwan Zungeru a jahar Neja sun tafi kotu domin neman a dakatar da aikin har sai anbiyasu diyyar gonaki da gidajensu.
Masu zabe a Kasar Ghana da ke Afirka ta Yamma sun fita zuwa runfunan zabe domin zaben shugaban kasa.
A yau laraba ake gudanar da babbar haduwa ta karshe ta wadanda suka kubuta da rayukansu daga farmakin da kasar Japan ta kai kan tashar jiragen ruwan Pearl Harbor a Hawaii, shekaru 75 cur bayan wannan harin da ya sa ita ma Amurka ta shiga cikin yakin duniya na biyu.
Shugabannin ma’aikatun tsaro da samar da bayanan sirri daga kasashe takwas na yankin SAHEL da SAHARA mambobin kungiyar UFL sun fara gudanar da wani taro a jamhuriyar Nijar, yayin da kungiyar mai alhakin tattarawa da musanyar bayanai a tsakanin wadannan kasashe ke cika shekaru 6 da kafuwa.
Yau Labara ne mutanen kasar Ghana ke fita rumfunan zabe domin zabar sabon shugaban da zai mulkesu a kasar.
Sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar kan batun hana shigowa da motoci ta kan iyakokin kasar wadda zata fara daga ranar daya ga watan shekara mai zuwa abu ne da wasu ke yabawa dashi, a yayin da wasu kuma ke bayyana hukuncin da cewa matakine na hanasu sana’arsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar bakwai ga watan Disamba don tunawa da kuma bunkasa harkar sufurin jiragen sama na fararen hula.
Shugaba Francoise Hollande ya zabi ministan harkokin cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve a matsayin wanda zai maye gurbin Fira Ministan kasar.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Japan ya ce firayin minista Shinzo Abe ba zai nemi gafara game da harin da Japan ta kai kan tashar jiragen ruwan Pearl Harbor ta Amurka a shekarar 1941 ba, a ziyarar da zai kai tsibirin Hawaii a cikin watan nan.
A wajen ginin hada-hadar kasuwancin Trump, inda layin 5th avenue da 56th street suka hadu a birnin New York, an ji hayaniya da sanyin safiyar yau, yayin da masu goyon bayan a sake kirga kuri’un jihohi 3 suka hadu da ‘yar takatar jam’iyyar Green Party, Jill Stein a wani gangamin tabbatar da cewa babu magudi a kirgan kuri’un da akayi.
Hukumar Kwastam ta Najeriya tace daga ‘daya ga watan Janairun shekara mai zuwa zata hana shigowa da motoci ta kan iyakokin kasar, sai dai a rika shigowa da su ta tashoshin jiragen ruwan Najeriya
Yayin da dakarun Najeriya ke ci gaba da kwato dukkanin yankunan dake hannun mayakan Boko Haram a jihohin Adamawa, Borno da kuma jihar Yobe, yanzu haka hukumar samar da wutar lantarki ta fara samar da wuta a wasu yankunan da aka kwato.
Domin Kari