Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Am Kaddamar Da Aikin Sa Ido Akan ‘Yan Sanda Masu Zirga-zirga A Nijar


Hukumar yaki da cin hanci a Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani aikin zuba ido akan ayyukan ‘yan sandan kula da zirga-zirga da nufin tantance zahirin abubuwa irin na cin hanci da ake zargin su da aikatawa.

Anyi hakan ne da nufin tantance zahirin abubuwa irin na cin hanci da ake zargin sun wakana a tsakanin ‘yan sanda da masu ababen hawa a ci gaba da neman hanyoyin murkushe wannan haramtacciyar dabi’a da ta shafi dukkan fannoni na rayuwa a kasar.

Yawaitar koke koken jama’a dangane da yadda wasu daga cikin jami’an tsaro suka mayar da aikin kula da sha’anin zirga-zirga tamkar wata hanyar samun kudi a hannun wadanda aka samu da laifin taka doka ya sa hukumar yaki da cin hanci HALCIA da hukumar ‘yan sanda kaddamar da wannan shiri na hadin guiwa domin gano gaskiyar lamari a cewar darektan sashen kula da bincike a hukumar HALCIA Cap Samaila Alhaji Issoufou.

Tuni dai aka baza jami’ai a wasu mahimman wurare nan birnin Yamai domin zuba ido akan mu’amular masu ababen hawa da ‘yan sanda a karkashin wannan tsari .

Yaki da cin hanci wani aiki ne da tun farko ya wajaba a wuyan ‘yan sanda inji mataimakin shugaban hukumar ‘yan sandan jihar Yamai Abdou Ibrahim a yayin bukin kaddamar da wannan shiri.

Ya ce hukumar ‘yan sandan farin kaya ke da alhakin kula da dukkan wani rahoton binciken da ya shafi ayyukan hukuma, haka kuma hukumar ‘yan sanda kan bi diddigin dukkan wani zargin cin hancin da ya shafi jami’anta. Kuma idan aka gano kamshin gaskiya ta kan dauki hukuncin da ya dace akan irin wadannan baragurbin jami’ai kuma ya ce haka su ke da wasu matakan riga kafin cin hanci a aikin ‘yan sanda.

Yaki da cin hanci wani abu ne da ke bukatar gudunmowar kowa don ganin an cimma nasarar matakan da hukumomi ke dauka inji Cherif Issouhou na kungiyar Transparency International.

Hukumar HALCIA da hukumar ‘yan sanda sun bayyana shirin fadada wannan aiki na zuba ido akan mu’amular ‘yan sandan zirga zirga da masu ababen hawa zuwa sauran jihohi a nan gaba kamar yadda shirin zai shafi sauran sassan da bayanan kuri’ar jin ra’yin jama’a suka bada damar gano alamomi masu kama da cin hanci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Am Kaddamar Da Aikin Sa Ido Akan ‘Yan Sanda Masu Zirga-zirga A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


XS
SM
MD
LG