Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Dan Fafutukar Kare Hakkin Bil Adama A China


Sun Wenguang, dan fafutuka

Sun Wenguan, wani farfesa ne da ya yi ritaya daga wata jami’a a lardin Shandong dake arewa maso gabashin China, wanda ga dukkan alamu hukumomin China suka tsare shi yayin da yake wata hira tarho da Muryar Amurka a makon da ya gabata.

A halin yanzu an fidda shi daga wani otal din sojoji inda ake tsare da shi zuwa wani wurin da ba a sani ba, a cewar wani jami’in otal da yake hira da sashen harshen China na Muryar Amurka da safiyar yau Lahadi.

A ranar Alhamis wata majiya ta fadawa Muryar Amurka cewa ana tsare da farfesan mai shekaru 84 a duniya a tsaunin Yanzi dake yankin Jinan na sojojin kasar.

An kama farfesan ne a ranar Laraba yayin da yake bada ra’ayinsa a kan shirin telbijin Muryar Amurka na harshen China, inda ya caccaki manufofin gwamnati a kan harkokin waje da na diflomasiyarta game da Afrika. A cikin hirar Sun ya fadawa Muryar Amurka cewa hukumomi na kokarin karya kofarsa su shigo masa a cikin gida domin su hana shi sukar gwamnati.

A hira da wata majiyar ta otal, wakilin Muryar Amurka ya gano hukumomi sun fitar farfesan daga inda ake tsare da shi kwanaki biyu da suka wuce zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Hukumomin China sun ki bada bayani a kan dalilin tsare farfesan. Muryar Amurka ta yi kokarin tattaunawa da ofishin hulda da jama’a na ma’aikatar harkokin wajen China domin jin ta bakinsu, amma lambar salula da jama’a ke kirar ma’aikatar akai na rufe kana kuma ba a daukar wayar tarhon.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG