Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INDONESIA : Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane


Ruwa
Ruwa

Rahotanni da dumi duminsu sun bayyana cewar an sami ambaliyar ruwa a kasar Indonesia wadda ta hallaka jama'a da dama.

Jami’ar kasar Indonesia sun ce a kalla mutane 17 ne suka mutu, yayinda har yanzu mutane uku suka bace bayan wata ambaliyar ruwa da aka yi kusa da wani wurin yawon bude ido a kasar.

Wata tawagar daliban jami’a su saba’in da kuma jagororinsu suna ziyarar wata mahadar ruwa ta Dua Warna dake arewacin Sumatra lokacin da ruwan yayi ambaliya a daya daga cikin makwararin ruwan.

Masu aikin ceto rayuka suna kan kokarin neman wadanda suka bace.

An saba ganin irin wannan tumbudin ruwan a lokacin tashin koramar ruwa a Indonesia dake lafawa a watan afrilu galibin shekaru.

XS
SM
MD
LG