Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Marabci Takwaran Aikinsa Na Faransa, Macron


Batutuwan Siriya da cinikayya na cikin abubuwan da ake sa ran shugabannin biyu zasu tattauna a ganawar da za su yi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da zuwan shugaban Faransa Emmanuel Macron, da wani shagali yau Talata a fadar White House kafin shugabannin biyu su gana kuma su halarci wata liyafar cin abincin dare.

Ana kyautata zaton bikin maraban zai kunshi kusan jami’an soja 500 daga sassan rundunar sojan Amurka 5, a yayin liyafar cin abincin dare ta farko da Trump zai yi a fadar da shugaban wata kasa, wata kungiyar mawakan birnin Washington ce zata nishadantar da su a lokacin liyafar.

Tattaunawar ta yau Talata za ta zo ne da batutuwa da yawa masu muhimmanci a fadin duniya da kasashen biyu ke fuskanta, ciki harda batun yakin da ake yi a Siriya, da shirin makaman nukiliyar Iran da kuma shirin Trump na sanya karin haraji akan karahuna da dalmar da ake shigowa da su daga wasu kasashen.

Trump na tunkaho da kawancen shi da Macron, kuma wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa ya gayyato shugaban na Faransa ya zama bakonsa karon farko zuwa Amurka a karkashin gwamnatinsa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG