Yau Alhamis ake sa ran sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai isa Berlin, domin ganawa da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da nufin duba hanyoyin da za'a bi a kawo karshen tarzomar da zuwa yanzu ta halaka yahudawa takwas da Falasdinawa kusan 50.
Mr. Kerry yace "abunda muke so mu gani shi ne matakai da ake dauka, walau ta baki ko a aikace, da zasu rage zaman dar dar, sake maido zaman lafiya, da kuma kawo karshen mummunar tarozmar" kamar yadda kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka John Kirby ya fada jiya Laraba.
Sakatare Kerry yana kuma shirin zai gana da shugaban yankin Falasidun Mahmud Abbas a Jordan a karshen mako.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya fada jiya Laraba cewa "bashi da kwarin gwuiwa" bayan da ya tattauna da shugaban Isra'ila da na Falasdinawa. Yayi kira ga duka sassan biyu su kai zuciya nesa, idan ba haka ba lamarin zai zame babbar tarzoma ko haddasa bori daga Falasdinawa.
Ahalinda ake ciki kuma, Firayim Minista na Isra'ila Benjamin Netanyahu yana kokarin kwantarda hankula sakamakon kalaman da ya furta cewa wani tsohon shugaban yankin Falasdinu ne ya iza Hitler ya yiwa yahudawa kisan kare dangi.