A lardunan Oromia da Somali mutane kusan 32 ne suka mutu sakamakon tashe-tashen hankulan da yankunan suka yi fama dashi.
Wata Yarinya 'yar kunan bakin wakre tayi dalilin mutuwar mutane biyar kana wasu da dama sukarasa rayukan su,wannan ya biyo bayan tada bomb din da tayi damara dashi ne.Ta tada wannan bomb din ne da a cikin wani masallaci dake cikin kasar Cameroon.
Sakataren Majilisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace kashe 'yan jinsin Rohingya da akeyi wannan wani yunkurin kakkabe su daga doron kasa
Ana ci gaba da yin Allah wadai da rikicin Burma da ya ki ci ya ki cinyewa, inda rahotannin ke zargin cewa ana aikata kisan kare dangi akan tsurarun Musulmi 'yan kabilar Rohingya.
Hukumomin tsaro sun tsare wani Alhaji Dan Nigeria sakamakon daukar wani abinda ya tsinta a harabar Harami
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa yabi sahun 'yan Nigeria wajen bayyana raayoyin su game da ficewar Nigeria daga cikin fatara
'Yan Nigeria naci gaba da bayyana raayin su game da yiwa majilisar ministocin Nigeria garanbawul musammam ma ganin kalaman da daya daga cikin su tayi kwanan nan
An gudanar da taron fahintar juna tsakanin manoma da makiyaya a masarautar Kontagora dake cikin jihar Niger.Fadar Mai martaba sarkin Sudan ne ta dauki nauyi wannan ganawar domin a samu fahitar juna.
An samu karin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da aka samu a kasar Mexico,Domin yanzu adadin yakai 90.
An dakatar da bude wuta a Rohingya, domin kaytan agaji su isa ga bayin ALLAH da wannan tashin hankalin ya rutsa dasu.
Mahaukaciyar guguwar nan ta Irma naci gaba da banna Jihar Florida, domin a jiya lahadi ta fantsamo tayi kaca-kaca da wannan jihar mai yawan mutane anan Amurka.
Jihohi 15 ne na Amurka suka kai karar Shugaba Donald Trump akan maganar rushe shirin DACA da aka samar zamanin mulkin shugaba Barrack Obama.
Shugaba Myanmar,Aung San Suu Kyi tace jamaa na kara gishiri cikin labarin tashe-tashen hankulan dake faruwa a kasar ta.
Shugaban Amurka Donald Trump yace akwai sauran lokaci kafin ayi tunanen daukar matakin da ake jin ya dace game da kasar Korea ta Arewa
Har yanzu a jihohin kudu maso yammacin Najeriya ana ci gaba da samun cece kuce game da batun shirin sake kame shugaban kungiyar neman sabuwar kasar Biafra wato Nnamdi Kanu
Biyo bayan hirar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yayi a sashen Hausa na Muryar Amurka yasa wani jigo a jamiyyar mayar masa da martani
Fara tayi wa manoma a Malbaza dake cikin jihar Tawa a junhuriyar Nijer mummunar barna, kuma maganin da ake kashe wadannan farin ya fara karewa
Ministar harkokin kasar waje ta Indonesia, Retno Marsudi, tana ziyara a kasar Myanmar domin ganawa da jagabar al’ummar kasar Aung San Su Kyi, da kwamandan rundunar sojan kasar, da kuma babban mai baiwa shugaban kasar shawara a harkokin tsaro.
Bayan ce-ce-ku-ce da aka yi ta yi tsakanin bangaren shari'ar Kenya da gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta, hukumar zaben kasar ta ce a watan Oktoba mai zuwa za a sake zaben shugaban kasar da kotun koli ta soke.
Amurka ta ce shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya kusa kure hakurinta duk da cewa ba wai Amurkan na son tsunduma cikin yaki ba ne, kamar yadda Jakadiyar kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta fada.
Domin Kari