An kashe wasu sojojin Amurka biyu a bakin daga, a wani al'amarin da ake ganin irin harin nan ne na sojoji masu canza sheka.
Shugagan Amurka Donald Trump na cigaba da dulmuya cikin abin da masu sukarsa ke kira take-taken nuna banbancin launin fata, inda ya auna birnin Baltimore mai rinjayen bakaken fata, da kuma wani fitaccen mai wakiltar birnin a majalisar dokokin tarayyar Amurka mai suna Elijah Cummings,
Yayin da ake cewa 'yan bindigar Zamfara sun gudu zuwa wasu jahohi saboda jami'an tsaro sun takura su, sai kuma gashi ana ta samun rahotannin da ke nuna alamar ba su gudu ba. Hasali ma, sai cigaba da gallaza ma jama'a su ke yi.
Kamar yadda ya ke a kowani watan azumin Ramadan, malamai na cigaba da bayyana ma jama'a abubuwan da su ka wajaba, da wadanda su ka haramta ga mai yin azumi. Anan mu na tafe ne da bayani kan yadda azumi ya shafi rukin mutane daban-daban.
A cigaba da yaki da 'yan ta'adda da sauran 'yan bindiga da kasar Saudiyya ke yi, ta ba da sanarwar cewa sojojjnta sun hallaka wasu mayaka 8 a Qatif wadanda ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne.
Kamar yadda wasu kwararru su ka yi ta hasashe a baya, tattaunawar Amurka da China ta kasa kaiwa ga cimma jituwa a bangaren cinakayya. Hasali ma kasashen biyu sun koma bakin daga, kuma sun fara bugawa a fagen kasuwanci.
A wani al'amari da ka iya farfado da tankiyar Amurka da Koriya Ta Arewa, Shugaba Kim Jong Un ya ba da umurnin gudanar da gwajegwajen muggan makamai, wanda hakan ya saba ma wata yarjejjeniyar da aka cimma.
Yayin da duniya ke kiran bani-Yahadu da 'yan kawunnensu, Falasdinawa, su kai zuciya nesa, abin sai dada faskara ya ke yi. Luguden wuta kan juna sai abin da ya karu, yayin da rayuka ke kara salwanta baya ga asarar dukiyoyi daga bangarorin biyu.
Kamar yadda aka yi ta fargaba a baya cewa hakan na iya faruwa, cutar Ebola, wadda ta sake barkewa a kasar Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta fara sake zama bala'i, inda tuni ta kashe mutane sama da dubu daya.
Al'ummar Fulani a kudu maso gabashin Najeriya sun musanta zarginsu da ake da kashe wasu 'yan kabilar Ibo shida. Su ka ce su ne ma aka fi kwara a tankiyar da aka yi ta sama tsakaninsu da wasu matasan Anambra-West.
Bayan da aka kusa samun tashin hankali a Gombe da safiyar jiya Asabar, hukumomi a Gombe sun yi maza sun kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe uku na yamma zuwa kafe shida na safe.
Yayin da ake cigaba da samun matsalolin tsaro a Janhuriyar Nijar, wata gamayya ta jam'iyyun 'yan adawa ta yi gangami a birnin Yamai, inda ta bukaci gwamnati ta tashi haikan wajen tabbatar da tsaro da inganta yanayin rayuwa.
A ranar Litinin masu zanga-zangar da kansu su ka rika aikin duba ababen hawa a kan hanyoyin da ke inda su ka yi tunga, a hedikwatar sojin kasar da ke birnin Khartoum.
Amma shugaban kasar da rukunin kamfanoninsa, sun fada a karar da su ka shigar ta hadin gwiwa cewa, “sammacin bayyana irin wadannan bayanan abu ne da bai yiwuwa, saboda ba abu ne da ya shafi harkokin majalisa ba.”
Yadda aka yi amfani da kwarewa wajen tsara wadannan jerin hare-hare guda takwas, wadanda aka auna su kan majami’u da otal-otal, ya girgiza kwanciyar hankalin da aka shafe shekaru wajen 10 ana mora a wannan kasa.
Jama'ar birnin Gombe sun ga wani abin tashin hankali bayan da wasu bugaggu da giya, wadanda ake kyautata zaton jami'an tsaro ne ma, su ka markade 6 daga cikin mambobin kungiyar BB da ke macin Easter a birnin Gombe.
'Yan makwanni bayan ayyana Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya sake cin zaben gwamnan jahar Sakkwato, jam'iyyar APC ta fara kuruwar cewa an fara ma 'ya'yanta bita da kulli.
Shugaban na Amurka, ya fada ta kafar twitter cewa, da Mueller da Atoni-Janar din Amurka William Barr, bisa ga binciken da Mueller ya yi, sun yi ittifakin cewa babu wani hadin baki, kuma babu wani karen-tsaye ga shari’a da ya faru.
Wutar, wadda a wani lokaci sai da ta yi sama da tsawon mita 10, ta lalata akasarin rufin majami’ar inda har hasumiyar rufin ta fadi.
Domin Kari