Bunkasar birane a 'yan shekarunnan na daga cikin matsalolin da ke raba manoma da makiyaya da filayensu a fadin Nijar. Game da wannan batun ne kungiyoyi tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar ne suka shirya taron domin neman mafita.
Sakamakon tashe-tashen hankulan da ake samu a cikin kasa ne yasa ‘yan Najeriya ke bayyana ra'ayoyinsu akan yadda za a samu zaman lafiya cikin kasa.
An sace wasu jami'an gwamnatin Kamaru yayin da aka kashe wasu sojoji a ranar bikin matasa a yankin da ake magana da harshen ingilishi a arewa maso kudancin kasar.
Fulani a jihohin da aka fara anfani da dokar hana kiwo barkatai sun koka akan irin halin da suke ciki, sun bukaci gwamnatin tarayya tayi wani abu akai.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido yace duk wani dan Najeriya nada 'yancin tsayawa takara kuma 'yan Najeriya sune zasu yanke hukunci
Kungiyar G-5 a yankin Sahel tana gudanar da taro a jamhuriyar Niger, da zummar inganta matakan tsaro da samar da ayyukan yi ga matasan kasashen ta.
Rundunar sojan Najeriya tace duk da cewa bata kwato daukacin 'yan matan chibok ba, duk da haka ta sami nasarar kubutar da mutane sama da dubu 30 daga hannun 'yan Boko Haram.
Kotun koli ta yanke hukuncin mika garin Piyame ga wani attajiri mai suna Kabulu Fada bayan an jima ana tafka sharaa game da mallakar wannan garin.
Duik da ikirarin da gwamnatin jamhuriyar Nijar keyi na cewa ta kakkabe boko Haram har yanzu da sauran rina a kaba
Shugaban kungiyar bunkasa ci gaban fasahar sadarwa mai suna CITAD tace kowane dan Najeriya na da rawar da zai taka domin samar da zaman lafiya cikin kasa.
An bukaci 'yan kasuwa da su rika kula da kashe hasken wutan lantarki a duk lokacin da zasu rufe shagunansu domin gujewa tashin gobara.
Matasa 350 daga jihohi 10 na Najeriya zasu amfana da shirin horaswar aikin gona kyauta domin yaki da rashin aikin yi.
Kungiyar boko haram takai hari a garin Shatemeri dake cikin jamhuriyar Niger har ta kashe dan karamin yaro guda.
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta ce zata tabbatar an bi dokar hana kiwo barkatai.
Ganawar da Shugaba Buhari yayi a bainar jamaa shida tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta nuna cewa suna siyasa bada gaba ba.
A kokarin ganin tattalin arzikin kasarsa ya bunkasa, shugaban Liberiya George Weah ya rage ma kansa albashi da wasu alawus-alawus
An kashe wasu mutane uku a yankin Basa dake cikin jihar Filato amma sai dai ba a gane ko su wanene suka aikata wannan danyen aikin ba
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yace dokar hana yawo da dabbobi a cikin jihar na nan daram.Yace an samar da dokar ce ba domin rukunin wasu mutane ba,amma ga dukkan 'yan jihar.
Matasa a garin Zing a cikin jihar Taraba sun kona caji ofis yayin wata zanga-zanga dasuka yi
Daliban Jami'ar Damagaram da ke cikin jamhuriyar Nijar sun ce muddin ba a shawo kan matsalar da ke addabar jami'ar ba, to ba za su bari ma'aikatan jami'ar su ci gaba da aiki ba.
Domin Kari