Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata samar da ababen more rayuwa ga garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.
Kasar Sudan ta rike wasu 'Yan jarida domin binciken su akan rahoton karin farashin kayayyakinmasarufi da ya haifar da zanga-zanga.
Ga bisa dukkan alamu an kusa kawo karshen cutar kurkunu a nahiyar Africa, domin cibiyar yaki da wannan cutar ta jimmy carter tace kasashen Habashada Chadi kawai suka rage da wannan cutar.
Yau Asabar mataimakin shugaban kasar Amurka ya fara rangadin kasashe hudu a gabas ta tsakiya
Hukumar Zabe mai zaman kanta na Nigeria tace tayi wa mutane dubu casain rajista a jihar Niger
Gwamnatin Kamaru tace zata gudanar da zabubbuka hudu a cikn wannan shekarar.Kuma tuni ta fitar da kudi har Cfa miliyan 50 domin gudanar da wannan aikin.
Kungiyar Izalatul Bidia waikamatus sunna (JIBWIS) da hadin gwiwar wata kungiyar da ake kira TOLORAM daga kasar India suna bada kyautar hannu da kafar roba kyauta a Abuja
Gwamnatin jihar Nassarawa tace zata ci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira, kuma gwamnan yace zai tabbatar sai an inganta matakan tsaro a yankin da suke
kungiyar Boko Haram ta kai hari a garin Pallem, kuma sun kashe mutane kana sun kone babban asibitin garin
'Yan jarida a jamhuriyar Niger sun koka akan yadda jamian tsaro ke takura musu a lokacin da suke gudanar da ayyukan su.
Yayin da akakammala shirin bikin mika mulki ga sabuwar gwamnatinkasar Liberia, tuni har majilisar wakilan kasar ta fara aiki bayan ta zabi sabon shugaban.
Yanzu haka an bude wasu bakin iyakokin Nigeria da Jamhuriyar Cameroon, kuma har an fara kasuwanci a wadanan wuraren.
Anaci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a kaar Tunisia, wanda akayi irin sa a shekaru 7 da suka gabata.
Jam'iyya mai mulkin kasar Liberia ta ce ta kori shugabar kasar mai barin gado,Ellen Johnson Sirleaf, domin ta ki ta marawa mataimakin shugaban kasar baya a zaben da aka kammala kwanan nan.
Gwamnatin kasar Iran tace ba zata mutunta wani sabon yarjejeniya ba, sabanin wanda aka cimmawa da ita da Amurka dama sauran Manyan kasashen duniya.
Binciken wasu hukumomin Majilisar Dinkin Duniya da suka yi sunce sun gano 'yan kasar Syria dake gudun hijira a kasar Lebanon suna zama cikin mawuyacin hali.
Sama da dala biliyan 18 gwamnatin shugaba Donald Trump ke bukata a cikin shekaru 10 domin gina katangar da ta yi iyaka da Amurka da kasar Mexico.
Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa sufeta janar na 'yan sandan Nigeria umurnin ya koma jihar Benue da zama har sai tsaro ya inganta a jihar
Dalibai a Jihar Damagaran da ke Jamhuriyar Nijar sun bukaci gwamnati ta gaggauta biyan kudin alawus-alawus dinsu ko su dauki matakin da suke jin ya dace.
Wasu matasa daga kasashen Afirka sun kafa kungiya domin bunkasa harshen Hausa a cikin nahiyar ta Afirka.
Domin Kari