Kotun daukaka kara na nan Amurka tace umurnin hana wasu kasashe wadanda galibin su musulmai shigowa nan Amurka umurni ne da yafi karfin sa
An cimma matsaya tsakanin masu ruwa da tsaki na samar da zaman lafiya a kasar Sudan Ta Kudu.An cimma wannan matsayar ce a kasar Adis Ababa bayan an dauki lokaci mai tsawo ana tafka muhawara.
Yanzu haka shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fara wata ziyarar kwanaki biyu a Jamhuriyar Nijar inda zai gana da sojojin kasarsa da ke aikin wanzar da zaman lafiya.
Jami'an tsaro a kasar Australia sun kama wani haifaffen dan kasar Korea ta Arewa da suke zargi da gudanar da ayyukan leken asiri.
Wasu yan taadda sun kai wa wani wurin ibadan kirista hari har suka kashe mutane 8 kana wasu da dama suka samu rauni
Jam'iya mai mulki a Afirka ta Kudu za ta zabi sabon shugabanta, zaben da ake ganin zai iya kawo rikici a cikin jam'iyar wacce tuni take fama da matsalar rarrabuwar kawuna.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bukaci Korea ta Arewa data jingine batun ta na sarrafa makamai masu linzami muddin tana son a tattauna da ita.
Shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun gaza cimma matsaya akan batu bakin haure.Hakan ko ya biyo bayan taron da kungiyar tayi ne Brussel.
Kungiyar tarayyar kasashen larabawa ta bukaci sauran kasashen duniya da suyi watsi da matsayin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka game da kasar Falesdinu da Izraela.
An gudanar da Faretin murna a babban kasar Iraqi domi murnar korar kungiyar IS a cikin kasar kana an ayyanayau lahadi a matsayin ranar hutu.
Kasar Zimbabwe ta samar da kasafin kudin shekarar 2018 da yakai har dalar Amurka Biliyan 5, tace kuma zata tabbatar ta yi dokar da zai janyo masu saka hannu jari.
Kasar Iraqi ta bayyana cerwa tayi nasara fatattakar kungiyar IS da ta jima tana zame mata barazana.Prime Ministan kasar neHaider Al-Abadi ya bayyana haka a wajen wani taron da manema labarai suka shirya.
Shugaba Trump ya bude gidan adana kaya da kuma bayanan tarihi a Mississipi, inda ya yaba wa shugabannin da suka gabata wadanda suka taka rawar gani wajen yaki da wariyar launin fata anan Amurka.
An fara zabe a kasar India, amma akasar Hoduras ko 'yan adawa ne suka bukaci a soke zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan jiya
Ana iya cewa an fara samo bakin warware matsalar dake tsakanin Korea ta Arewa da Majilisar Dinkin Duniya, domin ko sun amince su rika tattauna lokaci-lokaci
Mutane 6 ne aka kashe akan iyakar Najeriya da Kamaru a lokacin da 'yan awaren masu magana da harshen ingilishi suka yi kokarin kai wa jami'an tsaron kasar ta Kamaru hari.
Wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane 6 kana wasu 13 sun samu rauni a Afghanistan sai dai ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin.
Ana iya cewa an samu rudani ko kuma bayanai masu karo da juna daga kalaman shugaba Donald Trump na dalilin da yasa ya kori tsohon mai bashi shawara a harkokin tsaro
An kori daya daga cikin masu aikin binciken kwamitin da Robert Mueller kewa jagoranci game da alakar tsohon mai baiwa shugaba Trump shawara a harkokin tsaro da Rasha.
Ansa dokar hana fita a kasar Hundarus domin jamiaan tsaro su samu damar shawo kan masu zanga-zanga sakamakon zaben da akayi a kasar a cikin satin data gabata.
Domin Kari