Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta fito da wani shiri na adashin zuwa aikin hajji ga maniyyatan kasar, inda za su dinga adana kudi kadan-kadan har su biya kudin kujera.
Kwalliya ta soma biyan kudin sabulu, a yayin da sabbin cefanen kungiyar Arsenal suka soma haskawa, a daidai lokacin da aka soma fafata gasar Premier ta Ingila.
Neymar ya dawo daga jiyyar cutar coronavirus, a yayin da kungiyarsa ta PSG ta ke shirin buga wasan farko ta bude gasar League 1 ta sabuwar kakar wasanni.
‘Yan kasar Rasha na gudanar da zabe a yau Lahadi, wanda ake sanya wa ido sosai saboda alamun rashin gamsuwa da babbar jam’iyyar United Russia, biyo baya zargin sanya guba ga shugaban adawa kuma malamin addini na Kremlin, Alexei Navalny.
‘Yan gudun hijira a Lesbos na tsibirin Girka sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin zaman su a sansanin gudun hijira mafi girma a turai na Moria, da wutar gobara ta lakume.
Naomi Osaka ta lashe babbar gasar Tennis ta US Open ta bana a bangaren mata, bayan ta yi galaba akan Victoria Azarenka a wasan karshe ta gasar a ranar Assabar.
China na kokarin shiga gaba wajen samar da rigakafin cutar coronavirus, a yayin da take kokarin yin amfani da rigakafin a siyasance domin daukaka martabar ta da matsayinta a duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da sanarwar cewa Daular Bahrain ta amince da Isra’ila a matsayin kasa, biyo bayan irin wannan yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa a watan da ya gabata.
Sojojin kasar Chadi 6 aka kashe a kusa da kan iyakar Libya da kuma kudancin yankin Tafkin Chadi, inda mayakan kungiyar Boko Haram su ke kai hare-hare, a cewar wasu jami’ai biyu.
Jami’ar George Washington ta Amurka tana bincike akan wata Farfesa a sha’anin tarihi, da ake zargin ta amsa cewa ta yi shigar burtu a zaman bakar fata ba bisa ka’ida ba a duk tsawon rayuwar aikin ta.
Tarkon Barcelona ya kama Lionel Messi, tilas zai ci gaba da buga mata wasa har zuwa karshen kwantaraginsa, yayin da babban amininsa Luis Suarez zai koma Juventus ya hade da abokin adawarsa Cristiano Ronaldo.
Shirye-shirye sun kankama na soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Afghanistan da 'yan Taliban, domin kai karshen yaki a karkashin jagorancin Amurka.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta karbi samfurin rigakafin cutar korona bairos daga Kasar Rasha saboda yakar wannan mugunyar cutar a kasarta.
Jami’an leken asirin Amurka sun daina yi wa majalisar dokoki bayani akan sha’anin tsaro ga zaben kasar, lamarin da ya janyo kakkausan martani daga ‘yan jam’iyyar adawa ta Demokrats.
Donald J. Trump, shugaban kasar Amurka na 45, kuma shugaba na 3 da aka tsige shi amma kuma ya sami kubuta, yana neman sake zabensa a wa’adin mulki na 2 a watan Nuwamba.
Abinda muka sani game da dan takakarar Shugaban kasa na Jam'iyar Democrat tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nada shugabannin sabuwar hukumar kula da masu larura ta musamman ta kasar.
Domin Kari