Al’ummomi Sun Rungumi Addu’a Kan Batun Tsaro

Alhaji Ibrahim Geidam

Al’ummomi da gwamnatocin yankin arewa maso gabas sun koma ga Allah don neman mafita game da matsalolin tsaron da yankin yake fuskanta.
Yayin da ake ci gaba da zullumi da juyayin sace dalibai mata da aka yi daga makarantar sakandare ta Cibok a Jihar Borno, al’ummomi da ma gwamnatoci na yankin arewa maso gabashin Najeriya su na kara dagewa da addu’o’i domin neman mafita daga wannan bala’I da ake fuskanta.

A wurin tarurruka na siyasa ko addini ko wani abu a yanzu a kan ware lokaci na musamman domin gudanar da addu’o’i a kan samun saukin wannan masifar tsaro dake addabar yankin da ma Najeriya baki daya.

Musamman ma, ana karfafa addu’a game da dalibai mata su fiye da 200 da aka sace tun ranar 14 ga watan Afrilu daga makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Cibok a Jihar Borno, wadanda har yanzu ba a kwato su daga hannun ‘yan bindigar da suka dauke su ba.

Gwamna Ibrahim Geidam na Jihar Yobe, ya jagoranci gudanar da irin wannan addu’a a lokacin da aka kaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar a Damaturu.

Gwamna Geidam yace a bayan addu’ar neman samun zaman lafiya, tilas a gudanar da addu’ar Allah Ya ceto wadannan dalibai mata Ya maida su gidajensu ga iyaye da ‘yan’uwansu cikin lafiya.

A bayan da aka jima ana gudanar da addu’a, gwamnan ya roki jama’a da su ci gaba da irin wadannan addu’o’I a cikin gidajensu, kuma duk inda wani malami yake, ya taimaka wajen addu’ar Allah Ya kubutar da wadannan dalibai.

Daga bisani dai an kaddamar da sabbin shugabannin na jam’iyyar APC kamar yadda wakiliyarmu Sa’adatu Mohammed ta aiko.

Your browser doesn’t support HTML5

An Rungumi Addu'a Don Maganin Matsalar Tsaro A Arewa - 2'46"