Accessibility links

Adadin Daliban Cibok na Karuwa ‘276’


Dalibai a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Bayan, a birnin Khartoum dake Sudan suna kira a nema dalibai mata da aka sace a Cibok. Mayu 2, 2014

Jami’ai a arewacin Najeriya sunce dalibai mata su 276 aka sace daga makarantarsu a watan da ya wuce, wadanda ba’a san inda suke ba.

Ofishin ‘yan sandan Jihar Borno da jami’an bayanan sirri sun kara adadin kiyasin yaran da aka sace, suna cewa iyayen yara sun kai korafin cewa adadin da ake bayannawa yayi kadan.

Kwamishinnan ‘yan sanda Tanko Lawan yace akwai “matukar wahala”, wajen tantance taka-mai-mai dalibai nawa ne aka sace, saboda akwai daliban wasu makarantun a lokacin wadanda suma suke rubuta jarrabawar karshe.

An sace yaran ran 15 ga watan Afrilu a garin Cibok.

Akan danlin Twitter, jama’a dayawa sun bayyana takaicinsu akan yadda gwamnati take wa lamarin rikon sakainar kasha, tayin amfani da #BringBackOurGirls, biyo bayan martanin tafiyar hawainiya da jami’an Najeriya, a cewarsu suka yi. Wasu ma sunyi kira ga Shugaba Goodluck Jonathan akan yayi murabus.

Laraba da Alhamis dinna, jama’ar Najeriya sunyi zanga-zanga a Abuja da wasu wuraren domin kira ga gwamnati akan ta kara kaimi wajen gani an ceto wadannan daliban.

Jihar Borno na daya daga cikin jihohi uku da gwamnati ta kaddamar mata da dokar-ta-baci a watan Mayun bara, kuma sojojin Najeriya sunce sun dauki matakai domin murkushe kungiyar da aka fi sani da Boko Haram, amma har yanzu ana cigaba da kai munanan hare-hare.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG