Accessibility links

Ba’a Jin Shawararrmu – inji Sheikh Dahiru Bauci


Sheikh Dahiru Usman Bauchi

A lokacin da suke addu’o’i game da halin da tsaro ya shiga a Najeriya, ‘yan darikar Tijjaniyya a taron da sukayi a birnin Jalingo dake Taraba Lahadinnan, ta bakin jagoransu Sheikh Dahiru Bauci sun yi korafi akan watsi da gwamnati takeyi da shawarwarin da suke bayarwa gameda tsaron kasa.

Sheikh Bauci yace “ai ba’a jin shawararmu. Mu ba kowa bane wajensu, domin ainihin gida, idan dai ba gaskiya ta gina shi ba, to idan gaskiya tazo, ko zaure aka yi mata shimfida zata yarda ta kwanta.”

Malamin dan asalin Jihar Bauci yayi wa Najeriya addu’a.

“Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya a Taraba, Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya a Najeriya baki daya,” Sheikh Bauci yana addu’a, jama’a na amsawa da “amin”.

“Ubangiji Yace dukkan bala’i da ya sauka, akwai dalilinsa. Mutanen kasa su suka tsokano bala’i, bala’i ya sauka akansu,” a cewar Sheikh Dahiru Bauci.

Najeriya dai tana fama da matsalar rashin tsaro, tun bayan abkowar kungiyar da aka fi sani da Boko Haram a shekara ta 2009, kuma gwamnati na cewa tana aiki domin shawo kan matsalar, amma har yanzu kone-kone da kashe-kashen fararen hula bai tsaya ba.

A kwanakin baya ‘yan bindiga a arewa maso gabashin Najeriya, sun sace dalibai mata sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok a Jihar Borno, inda har yanzu ba’a kubutar dasu ba. Sojojin Najeriya sunce sun kubutar da yaran baki dayansu a baya, amma sun janye kalamunsu.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG