Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Daliban Cibok Kadai Aka Sace Ba


Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno yana ziyarar kasuwar garin Bama da 'yan ta'adda suka kona, Alhamis 29 Afrilu, 2013.

Kwamishinan ‘yan sanda Lawal Tanko ya tattauna da VOA Hausa kan kokarin tabbatar da yawan daliban da aka sace a Cibok da yadda jama’a zasu iya taimakawa wajen gano su.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, Lawal Tanko, yace ya zamo musu tilas su zauna su tantance adadin dalibai mata da aka sace daga makarantar sakandaren mata ta Chibok a ranar 14 ga watan Afrilu, a bayan da aka ci gaba da samun adadin da ya sha bambam na yawan daliban da suka bace.

A hirar da yayi da wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa wasu daga cikin daliban da aka sace ba ma daliban wannan makaranta ta Cibok ba ne, sun je su rubuta jarrabawa ne a makarantar a bayan da aka samu matsaloli a wuraren da ya kamata suyi jarrabawar.

Lawal Tanko ya roki dukkan iyayen da wannan abu ya shafa, da su mika wa hukumomin tsaro hotuna da sunayen ‘ya’yansu da aka sace, domin ya kasance ana da cikakken bayani na wadanda suka bata da wadanda suka kubuta da kuma dukkan wadanda ba a gano su ba.

Yace hotunan zasu taimaka musu wajen gano daliban.

Kwamishinan ya bayar da wasu lambobin da za a iya kira domin a ba hukumomi duk wani bayanin da zai iya taimakawa wajen samo wadannan dalibai da aka sace

Lambobin sune: 08075897377, 08081777309, 08036121490

Game da adadin da suke da shi na yawan daliban da aka sace, kwamishinan ‘yan sandan ya ce alkalumansu sun nuna cewa dalibai 276 aka sace. Daga cikinsu, yace akwai dalibai 53 da suka kubuto, sun dauki hotunansu kuma sun dauki jawabansu. Wannan yace yana nufin akwai dalibai 223 wadanda ba a gano su ba ke nan.

Amma yace wannan adadin, iyaye ne zasu iya tabbatarwa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG