Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu Fito Da Daliban Cibok – inji Jonathan


Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bada umarni ga manyan jami’an tsaron kasa akan suyi ‘duk abinda zasu iya yi’ domin ceto dalibai sama da 200 mata da aka sace a watan da yace.

A wata hira da aka nuna a kafofin yada labarai Lahadinnan, Jonathan yayi alkawarin “…duk inda matan suke, zamu tabbatar mun fito dasu.”

Shugaban ya bayyana lamarin a matsayin mai “juyayi” da “takaici,” kuma yayi kiran hadin kan iyaye, da ‘yan uwa da al-ummomi wajen ceto daliban.

An sace yaran ne ran 15 ga watan Afrilu, a garin Cibok dake Jihar Borno. Misalin 50 daga cikin 276 daga daliban da aka sace sun kubuto.

Ana dorawa kungiyar Boko Haram alhaki, amma har yanzu kungiyar bata fito ta dauki alhaki ba.

Wasu jami’ai sun bayyana cewa sun tabbatar an ketara da wasu daga cikin daliban iyakar Kamaru da Cadi.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG