Accessibility links

​Kungiyar tayar da kayar Baya, da aka fi sani da Boko Haram ta dauki alhakin sace daruruwan dalibai mata daga arewacin Najeriya a watan da ya wuce.

Wannan alhaki da kungiyar ta dauka, yazo ne a hotunan bidiyo da ta sakar wa kafafen yada labarai Litinin dinnan. A cikin bidiyon, Abubakar Shekau yace “Ni na sace matanku” sannan yayi alkawarin “zamu sayar dasu a kasuwa.”

‘Yan bindiga sun sace matan ne daga makarantarsu dake garin Cibok, a Jihar Borno ran 14 ga watan Afrilu. Jami’an Najeriya sunce wasu daga cikin yaran sun kubuto, amma misalin 276 har yanzu ba’a gansu ba.

A yammacin Lahadinnan, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya baiwa manyan jami’an tsaron kasa umarnin yin duk abunda zasu iya yi domin kubutar da daliban.
A wata ganawa da yayi da manema labarai a hotunan bidiyo, Mr. Jonathan yayi alkawarin “..duk inda matan suke, zamu fito dasu.”

A halin da ake ciki, ‘yan Sandan Najeriya sun kama shugaban masu zanga-zangar lumana dake neman gwamnati ta nemo daliban. Naomi Mutah Nyadar ta shiga hannun jami’an tsaro ne a yammacin Lahadinnan bayan ganawarta da matar Shugaban kasa.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG