Hukumar kula da kamfanonin wayar salula a Nigeria ta gargadi kamfanonin dake boye lambobin da ake kira daga kasashen waje da su daina, ko kuma su hadu da hushin hukumar
Shugaban Jam'iyyar adawa na kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, yace zaiyi murabus daga shugabancin jam'iyyarsu ta Movement For Democratic Change (MDC) saboda tsufa da rashin lafiya sun kama shi.
Rundunar 'yan sandan NIgeria tayi nasarar kame wasu 'yan fashin da makami dake fashi tsakanin Abuja da Kaduna
Koriya ta Arewa da KOriya ta gudu zasu gana akan batun wasan Olympic dama batun dangantakarsu.Abinda sguhaban Amurka Donald Trump ke cewa yana fata batrun ya wuce na Olympic.
Kasar Iran tace ta shawo matsalar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki anay a cikkin kasar.Mahukuntar kasar suka ce zasu gudanar da taro domin gano dalilin wannan bore take da hana aukuwar haka nan gaba.
Wani kanfanin Amurka yana gaba da binciken jirgin kasar Malasiya da yayi hadari a shekarar 2014
Hukumar zaben kasar Russia ta dakatar da shugaban 'yan adawa tsayawa takarar shugaban kasa wanda za ayi a cikin watan maris.
Shugaban Amurka da wasu Sanatocin jamiyyar su dama 'yanmajilisar zartarwa zasu gudanar da wani taro a Camp David
Matsalar man fetur da akeci gaba da fuskanta a Najeriya ya haifar da cece kuce tsakanin kanfanin samar da man na (NNPC) da majilisar Dattijai.
Wasu 'Yan Najeriya sun koka akan farashin kudin hasken wutar lantarki, sun bukaci gwamnati da ta yi wani abu a kai.
'Yan gudun hijirar da suka tsere daga Najeriya zuwa jamhuriyar Kamaru sakamakon hare-haren Boko Haram, sun bukaci a mayar da su garuruwansu na asali.
Sakamakon harin da wani dan kunar bakin wake yakai a gabashin kasar Afghanistan yayi dalilin mutuwar mutane har 15
Domin takawa masu zanga-zanga a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo birki, jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa masu boren.
Domin kare aukuwar ayyukan taadanci, mahukunta a birnin New York dake na Amurka sunce sun inganta matakan tsaro a dandalin Times Square inda za gudanar da bikin shigowar sabuwar shekara
Hukumomin bada agaji na Majilisar Dinkin Duniya sun koka na rashin samun damar kai kayan jin kai ga mabuta dake kasar Yemen
Wani dan bindiga yakai hari a wani coci dake birnin CVairo kuma ya kashe mutane 9 ciki ko harda dan sanda guda,kana mutane biyar sun samu rauni.
'Yan kasar Liberia naci gaba da murnan a babban birnin kasar ta Monrovia biyo bayan zaben sabon shugaban kasa George Weah
Kasar Korea ta Arewa tasa kafa tayi fatali da sabon kudirin sa mata takunkunmi da kwamitin samar da zaman lafitya na majilisar dinkin duniya tayi.
Kasashen da suka hada da Pakistan, China,Russia,Turkey,Afghanista,da Iran suna gudanar da taro a kasar Pakista domin duba yada zasu hada kai su yaki 'yan taadda.
An horas da daruruwan 'yan gudun hijira dake sansanin Minawoa sanaoin hannu.Wannan sansani dai na cikin jamhuriyar Cameroon ne.'Yan guduun hijirar zasu dogarada kansu idan sun koma garuruwan su na asali
Domin Kari