Gwamnatin tarayyar Nigeria tayi alkawarin sa kafan wando daya da duk wani ko wasu da aka samu suna marawa kungiyar 'yan taadda baya.Ministan Shara'a na kasar ne yayi wannan furucin sailin da yake zantawa da Muryar Amurka a Abuja.
Anaci gaba da kai ruwa rana tsakanin jamiyya mai mulki na kasar Uganda da kuma 'yan adawa akan kayyade shekarun tsayawa takarar shugabnan kasa.Domin ko jamiyyar na neman ta cire adadin shekarun tsaya takara dake cikin dokar kasar.
Ministan harkokin kasar waje na kasatr Venezuela yayi ALLAH waddarai da saka kasar cikin jerin wadanda ba zasu sha da dadi ba muddin suka yi yunkurin shigowa Amurka
Zaman lafiya ya dawo a jihar Abia inda aka kwashe kwanaki ana zaman dar-dar, wannan ne ma yasa Hausawa mazauna jihar suka bukaci 'yan uwansu da suka wuce Arewacin Kasar da su dawo.
Sojojin saman Nigeria sunce sun sake tarwatsa matattaran 'ya 'yan kungiyar boko haram,Sojojin suka ce sun hango su ne daga sama kuma zasu ci gaba da kai wannan harin sai sun tabbatar sun fasa garken su.
Shugabannin kungiyar Meyetti ALLAH da sarakunan Fulani a jihohin kudu maso yammacin Nigeria sun gudanar da taro a garin Ibadan, domi inganta zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
Har yanzu ba abada kuduin da za ayi anfani dasu ba wajen sake gina jihohin arewa maso gabashin Nigeria da yaki yadaidaita ba.
Wasu da ba asan ko su wanene ba sun harbe babban sojin kasar Somalia.Wannan lamari dai ya faru ne a babban birninkasar wato Magadishu.
Sojojin samar da zaman lafiya na majilisar dimnkin duniya dake aiki wanzarda zaman lafiya a kasar mali su uku ne suka rasa rayukan su kana wasu biyar suka samu rauni sakamakon fadawa kan wani bomb da aka dana bakin titi.
Angela Merkel ta sake yin nasarar a zaben da aka gudanar a kasar dta Jamus.Wannan dai shine karo na 4 tana lashe zaben, wanda rabon da a samu wanda yayi wannan nasarar tun bayan yakin duniya na biyu
Yanzu haka kasashen Chadi,Iran,Libya,Koriya ta Arewa,Sauran suneSomaliya,Venezuela da Yemen zasu fuskanci tsauraran sharudda kafin a bari su shigo Amurka.
Barayin mashin a jamhuriyar Niger sun bullo dawata sabuwar dabara,Barayin dai suna shaka wa mai mashin wani sinadari ne wanda har yanzu ana bincike akai domin gano ko wane irin sinadari ne.
An kashe wasu jami'an tsaro su biyu da rana tsaka a jamhuriyar Niger, sai dai an kasa gane ko wanene suka aikata wannan danyen aikin, amma jami'ai sunce suna nan suna gudanar da bincike
Gwamnatin jihar Borno ta bukaci nakasassu a jihar da su jingine sana'ar bara su rungumi sana'oi, kwamishinan mata da walwalasr matasa ne MadamPanta Baba Shehu tayi wannan kiran.
Aci gabada kokarin ta na samar da tsaro cikin kasa rundunar Sojan Nigeria ta horas da wasu jami'ain tsaron da ba sojoji ba.
Maaikatan tattara haraji a jamhuriyar Niger sun fara yajin akan abinda suka kira rashin gaskiyar da ake neman ayi musu.Sai dai hukumomin kasar basu ce kome ba game da wannan batu.
Maaikatan jinya da Ungozoma na barazanar fadawa yajin aikin da sai abinda hali yayi.Duk da yake sunce bason su bane su tsuduma cikin wannan yajin aikin amma shugabannin kungiyar sunce hakan zai zama tunatarwa ga gwamnati
Wata kungiya mai zaman kanta da hadin gwiwar 'yan jarida na tattaunawa akan hanyoyin da za abi domin inganta makarantun allo a arewacin Nigeria.
Kasar Jordan na daya daga cikin kasashen da tayi wa Nigeria alkawarin bata makamai, yanzu haka dai ta cika wannan alkawarin, saura kasar Saudi Arabia ita ma ta cika nata.Ministan Tsaron Nigeria Janar Mansir Dan Ali yayi wannan albishir din a zantawar su da Sarfilu Hashim Gumel.
A kokarin magance zaman kashe wando kungiyoyi masu zaman kansu suna koya wa mata da matasa aikin yi a jihar Bauchi.Kungiyoyin sunce suna samun nasarar wannan aikin ne domin suna samun tallafi daga hukumomin kasa da kasa irin su UNICEF.
Domin Kari