Domin samar da tsaro a Nigeria rundunar sojojin Saman kasar tafara wani aikin inganta matakan tsaro a kudu maso gabashin kasar, inda yanzu haka aka aika musu da wani jirgin jet domin wannan aiki.
Shugaban Amurka ya kwashe yinin ranar Litinin yana ganawa da shugabannin daban daban yayin da yake halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a karon farko inda zai yi jawabinsa a yau Talata.
Alamu sun nuna cewa kasar Iran ba zata mika wuya ba game da yarjejeniyar da aka cimmawa da ita a cikin shekarar 2015 game da shirin ta na makamin nuiliya ba, duk ko da matsa mata da Amurka keyi
An kama mutun na biyu da ake zargin kai hari a Birtaniya, wannan ne yasa mahukuntar kasar suka cean sassauta barazanare kai harin da kasar ke fuskanta
Kungiyar Hammas mmai gwagwarmaya da makami tayi ba zata jiya lahadi domi ta dauki matakin kawo karsgen rikici da take yi a siyasance.
An samu rarrabuwar kawuna cikin jamiyyar APC dake jihar Katsina.Wasu 'yan jamiyyar da suka gudanar da taron manema labarai a Kaduna sunce anyi yaki dasu amma an barsu da kutirin doki.
Wasu 'yanArewacin Nigeria dake zaune a kudu masoo gabashin Nigeria sun roki gwamnatin tarayyan kasar data yiwa ALLAH da maaikin sa ta kara yawan yawan jami'an tsaro a yankin na kudu maso gabas
Kungiyar nan da ake kira HED TAMAT a jamhuriyar Niger ta fara ran gadin ganawa da shugabanni al'umma musammam sarakuna domin samar da zaman lafiya a kasa.
Masana harkokin shara'a suna gudanar da taro a jihar Adamawa da niyyar lalubo hanyar da za a kawo karshen cin zarafin yara da mata. Mahalarta taron dai sun kunshi kwamishinonin shara'a ne na daukacin jihohin tarayyar Nigeria, kuma MInistan Shara'a Abubakar Malami ne ya bude taron.
Jami'an tsaro a jihar Delta sunce sunyi nasarar kame wasu mutane biyu da ake tuhuma da kaiwa wasu mutane hari a Asaba dake cikin jihar Delta.Jami'an suka ce suna nan suna ci gaba da bincike domin zakulo sauran wadanda ake tuhuma da kai wannan harin.
Wasu Lauyoiyi da masana harkokin tsaro a Nigeria sunce haramta kugiyar nan mai rajin kafa jamhuriyar Biafra yayi dai-daui da abinda dokar kasa ta tanada
Ga bisa dukkan alamu rigima na neman ta kunno kai a cikin kungiyar kwadago ta Nigeria, yayin da daya bangaren ke kiran ma'aikata su shiga yajin aiki, daya bangaren ko cewa yake yi ma'aikata suyi biris da wannan kiran.
Farfesa Ango Abdullahi Tsohon mai baiwa shugaban Nigeria Chief Olusegun Obasanjo shawara a harkokin noma yace lokaci yayi da 'yan Nigeria zasu dubi junan su su fada musu gaskiya.Yace a bar ganin lafin dokar kasa.Domin ba abinda ya samu dokokin Nigeria, illa masu sarrafa dokokin.
Wani jirgin ruwa yayi hatsari a cikin kogin shiroro dake cikin jihar Niger kuma mutane sama da hamsin ne suka rasa rayukan su.
Rundubar 'yan sandan Nigeria ta samar da wani gangamin wayar wa mutane da kai akan beli.Rundunar ta jadadda cewa beli kyauta ne don haka jama'a su kula.
Domin samar da hanyoyyin dakile anfani da hanyoyin sadarwa ta zamani wurin cutar al'umma, hukumar bincike ta kasar Jamhuriyar Niger ta samar da wani taro na musammam.
Sakamakon konewar tiransifoma, hakan ya haifar da karancin samar da hasken wutar lantarki a jihohin Bauchi, Gombe,da Plateau.
Aci gaba da kokarin wayar wa mutane da kai, Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nigeria, hukmar tayi wata ganawa da masu rubuce-rubuce a kafofin sadarwan zamani
Gwamnonin Arewacin Nigeria sunce ba zasu fidda matsayar su ba har sai sunji abinda jama'ar su ke bukata. Game da sake fasalin kasa.
An zabi kasar Paris domin ta dauki dawainiyar shirya wasannin shekarar 2024.Hukumar kula da wasannin motsa jiki ta duiniya ce tabada wannan sanarwan, yayin da tace a shekarar 2028 ko Los Angeles nan Amurka ne za a gudanar da wannan gasar.
Domin Kari