Kasar Saudiyya ta kame wasu jami'an gwamnatin ta hadi da wasu 'yan gidan sarauta kan zargin cin hanci da rashawa,wannandai ana yi ne da zummar samun daidait ga mulkin kasar.
Shugaban 'yan awaren kasar Spain ya mika kai shida wasu mutum hudu da suka gudu zuwa kasar Belgium, kuma suncea shirye suke su bada hadin kai.
Jami'an 'yan sanda a kasare Bangaladesh sunce wani jirgin kwale-kwale dake dauke da mutane 50 yan jindsin Rohingya ya tintsuure a cikin rafin NAF kuma da dama daga cikin su sun halaka.Su dai wadannan mutane suna kan hanyar suneta zuwa makwabciyar kasar Bangaladesh.
Sojojin Iraqi sun bayyana nasarar da suka yi na kamewasu muhimma wurare a matsayin abindazai kara durkusad da abokan gaban su
Wani tsohon babban kwamandar kungiya Al'shabab ya bayyana takaicin sa game da yadda wasu suka halaka mutane har kusan dari 3, Yace yana fata ALLAH yatona asirin wadanda suka aikata wannandanyen aiki.
Shugaban Amurka Donald Trump yace muddin 'yan jamiyyar Democrat naso su cimma matsaya dashi akan batun shirin DACA to wajibi a cimma wasu sharudda,
Mazauna yankin Catonia su gudanar da zanga-zangar lumana na ci gaba nuna kokari su na ballewa daga kasar Spain.Jam'a da dama ne suka fito wannan zanga-zangar wanda aka yi cikin kwanciyar hankali
Wasu 'yankabilar Rohingya su 12 sun halaka a ciki koginNaf bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife.Wadannanmutanen dai suna kokarin tsrewa ne daga kasar su zuwa Bangladesh.
Sojojin Iraqi sun yi nasarar kwato birnin Hawija da yake hannun 'yan kungiyar IS,Ministan kasar Haider Al-Abadi yace wannan nasrar bata kasar Iraqi bane kawwai na duniya ne baki daya.
Amurka ta bada tabbacin mutuwar sojojin ta biyu dake aikin samar da tsaro a Jamhuriyar Nige,Sai dai ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aiki.
Baya dage ziyarar da jami'an majilisar Dinkin DDuniya suka yi na ki ziyara Kasar Myanmar, yau tawagar ta isa kasar musammam a yankin da 'yan jinsin Rohingya suke
Prime ministan Thailand ya kawo ziyara a fadar white House kma sun tattauna da shugaba Donald TRump
Sakamakon wani hari da aka kai a Syria yayi dalilin mutiwar mutane 10 kana wasu da dama sun samu rauni
Shugaba Donald Trump yace ba makawa sai anyi wa tsarin ayyukan gwamnati kwaskwarima,Ga bisa dukkan alamu yana shagube ne ga sakataren lafiya Tom Price.
Kuria'ar neman cin 'yancin gashin kai da Kurdawan kasar Iraqi suka jefa baiyi wa gwamnatin kasar dadi ba.Yanzu haka dai majilisar dokokin kasar ta umurci Prime Minister Haider Al-Abadi da ya dauki mataki kan jefa wannan kuri'ar da kurdawan suka yi.
Fadar White ta aike da wani kudirin data ke neman samun damar rage adadin 'yan gudun hijira da zasu shigo Amurka.Gwamnatin ta shugaba Donald Trump ta nemi a rage adadin wadannan mutanen kwarai da gaske
Domin inganta zaman lafiya a jihar Niger kabilu daban-daban dake zaune cikin jihar sun gudanar da taron kara fahintar juna.
Domin habbaka ilmi tsakanin su,Jami'ar Maiduri a Nigeria da jamia'ar kasar Sudan Wacce take Birnin Khartoun na kasar Sudan sun kulla yarjejeniya.Wadannan jami'oin dai zasu rika musayar dalibai.Da sauran bayanai dake da nasaba da bincike.
Gwamnatin jihar Lagos ta kaddamar da cibiyar binciken kwayar halittar dan adam.Wannan zai taimaka kwarai da gaske wajen warware gardama game da duk wani abu dake da nasaba da jinsi.
Hukumar nan mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar Nigeria zagon kasa wato EFCC, ta gurfanad da wasu tsoffin jami'an gwamnatin jihar Adamawa, ciki ko harda tsohon kwamishinan kudi.
Domin Kari